Najeriya-Hushpuppi

An kaddamar da bincike kan Abba Kyari a badakalar Hushpuppi

Abba Kyari da Hushpuppi
Abba Kyari da Hushpuppi © Daily Post Nigeria

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kaddamar da bincike a game da zargin da ake yi wa mataimakin Kwamishinan ‘Yan sandan kasar Abba Kyari, wanda Amurka ke zargi da alaka da wani shahararren dan damfara Ramos Abbas da ake kira Hushpuppi da yanzu haka ke tsare a hannun FBI da ke Amurka.

Talla

Shi dai Hushpuppi, mai shekaru 37 a duniya, ya zargi Kyari da karbar makudan kudaden don kame wani abokin harkallarsa mai suna Kelly Chibuzo Vincent.

Sai dai tuni Kyari ya musanta wannan zargi a shafinsa na Facebook, yana mai bayyana cewa, bai karbi ko sisin kwabo ba daga hannun Hushpuppi.

Kyari na cikin zaratan jami'an 'yan sandan Najeriya da suka yi fice wajen yaki da miyagun laifuka a kasar, yayin da wannan batu na cin hanci da rashawa ya haifar da cece-kuce a sassan kasar.

Wata sanarwa da FBI ta fitar ta ce, Hushpuppi ya damfari mutane daban daban akalla Dala miliyan 24, ciki kuwa har da wata Dala miliyan 1.1 da wani attajiri ya ware domin gina makarantar kananan yara a Qatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI