Najeriya-Ambaliyar ruwa

Jihohin Najeriya 28 na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa

Ambaliyar ruwa a bana ta afka wa kasashen duniya da dama
Ambaliyar ruwa a bana ta afka wa kasashen duniya da dama VALENTINO DARIEL SOUSA AFP/File

Hukumar da ke Hasashen Yanayi a Najeriya, ta yi gargadi a game da yiyuwar samun ambaliyar ruwa daga watan Agusta zuwa Oktoban wannan shekara a jihohi 28 da ke kasar.

Talla

Hukumar ta gargadi jihohi da su dauki matakai don kauce wa samun asara kamar dai yadda hakan ta faru a shekarar da ta gabata, inda aka samu asarar rayukan mutane 155 yayin da sama da dubu 129 , ambaliyar ta shafe su.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Muhammad Kabir Yusuf daga birnin Abuja

 

 

Jihohin Najeriya 28 na fuskantar barazanar ambaliyar ruwa

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.