Najeriya-Zamfara

Zamfara: 'Yan bindiga sun sace ma'ikata 2 a babban asibitin Dansadau

Hoton 'yan bindiga somin misali.
Hoton 'yan bindiga somin misali. © India TV News / PTI

A Najeriya ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu ma’aiktan jinya biyu, bayan da suka kutsa cikin babban asibitin garin Dansadau dake karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a Najeriya.

Talla

Rahotanni daga garin na Dansadau sun ce da shigar ‘yan bindigar asibitin ne suka fara neman likitoci da ma’aikatan jinya, inda suke bi daki-daki da ofis ofis.

Sun kuma nufi gidajen ma’aikatan asibitin ko za su yi katarin gamuwa da karin likitoci ko ma’aikatan jinya da za su dauke, amma hakan bai samu ba.

Jaridar ‘Daily Trust’ da ake wallafawa a Najeriya ta ruwaito cewa tun da farko, ‘yan bindigar sun yi yunkurin kai wa kauyen Maigoge, mai nisan kilomita 6 daga garin Dansadau hari, amma ‘yan sa kai suka taka musu birki, inda suka kashe wasu, tare da raunata wasu.

Kauyen Maigoge ya yi suna wajen taka wa ‘yan bindiga birki, saboda yadda ‘yan sa kai suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare yankin nasu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.