Najeriya

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta dakatar da Abba Kyari

Abba Kyari, da Hushpuppi.
Abba Kyari, da Hushpuppi. © Daily Post Nigeria

Hukumar kula da ayyukan 'yan sandan Najeriya ta dakatar da wani babban jami’in ‘yan sanda Najeriya bayan da wani shahararren mai amfani da dandalin sada zumunta da ke fuskantar tuhumar aikata damfara  a Amurka ya bayyana cewa su kan gudanar da wasu ayyuka tare.

Talla

Ramon Abbas da ake wa inkiya da Hushpuppi, wanda ya amsa laifin aikata damfara ta intanet,  ya bayyana sunan mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Abba Kyari a matsayin abokin tarayya, lamarin da ya sa rundunar ‘yan sandan kasar su kaddamar da bincike.

Hukumar kula da harkokin ‘yan sanda a  Najeriya ta ce wannan dakatarwar da aka wa Kyari za ta ci gaba da aiki har sai hukumar FBI ta Amurka ta kammala bincike.

A ranar Laraba, hukumar FBI ta Amurka ta ce Hushpuppi ya yi damfarar kudi da ya kai dala miliyan 24 jimilla.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.