Najeriya-Korona

Najeriya ta samu tallafin alluran Korona guda miliyan 4 daga Amurka

Shubagan Najeriya Muhammadu Buahri.
Shubagan Najeriya Muhammadu Buahri. REUTERS - Siphiwe Sibeko

Najeriya ba karbi kunshin alluran rigakafin annobar Korona na kamfanin Moderna  guda miliyan 4  daga Amurka, a yayin da kasar ke kara azama wajen kokarin dakile yaduwar cutar da ta sake kunno kai  a karo na 3.

Talla

Jami’a daga ofishin asusun kula da kananan yara na duniya a Najeriya ne suka karbi wadannan alluran da suka isa kasar cikin jiragen sama 2, a filin tashi da saukan jiragen sama na Abuja.

Wannan ne karo na biyu da alluran rigakafin wannan shu’umin cuta ke isowa kasar da ta fi yawan al’umma a nahiyar Afrika.

A watan Maris, kasar ta karbi alluran rigakafi har guda miliyan 4, a karkashin shirin wadata matalautan kasashe da rigakafin Korona na COVAX.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.