Najeriya

Badakalar Hushpuppi: An maye gurbin Abba Kyari

An maye gurbin Abba Kyari da Tunji Disu.
An maye gurbin Abba Kyari da Tunji Disu. © naijanews.com

Gwamnatin Najeriya ta sanar da maye gurbin   Abba Kyari, wanda aka dakatar da shi , bayan da Hukumar bincike ta FBI dake Amurka ta zarge shi da hannu wajen cin hanci da rashawa.

Talla

Wanda aka nada yanzu da zai tafiyar da  aikin musamman na kai dauki na ‘Yan Sandan kasar shine DCP Tunji Disu.

A ranar Litinin kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya Frank Mba, ya fada a wata sanarwa cewa, sufeto Janar na ‘yan sandan kasar ya amince da nadin Mr Disu a ranar Litinin, tare da umurninn cewa ya kama aiki nan take.

Ya kara da cewa nadin nasa ya na zuwa ne sakamakon shawarar hukumomi na wajibcin cike gibin da aka samu na shugabanci a bangaren IRT na ‘yan sanda biyo bayan dakatarwar Abba Kyari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.