NIGERIA-LIKITOCI

Likitoci a Najeriya, sun shiga kwana na biyu na yajin aiki

Devant l’hôpital Ana Francisca Pérez de León 2 à Caracas.
Devant l’hôpital Ana Francisca Pérez de León 2 à Caracas. © Marie Normand / RFI

Likitoci masu neman kwarewa a Najeriya, sun shiga rana ta biyu da faran yaji a duk fadin kasar, lamarin da ya jefa marasa lafiya a cikin mawuyacin hali saboda rashin tabbas.Likitocin dai na wannan yajin aiki ne don neman a biya su wasu hakkokinsu da suka makale a hannun gwamnati, yayin da a hannu daya suke korafi a game da rashin kayan aiki.Wakilinmu a Abuja Muhammad Kabir Yusuf, ya zagaya a wasu asibocin don ganin halin da ake ciki, ga kuma rahoton da ya aiko mana.