Filato

Gwamnatin Filato ta ce kura ta lafa a birnin Jos

Wasu yankuna da matsalar tsaro ta tillastawa mazauna yankunan tsrewa daga gidajen su
Wasu yankuna da matsalar tsaro ta tillastawa mazauna yankunan tsrewa daga gidajen su Audu Marte AFP/Archivos

Gwamnatin Jihar Filato da ke Najeriya ta sanar da cewar jami’an tsaro sun yi nasarar mayar da doka da oda a Yankin Gada Biyu dake birnin Jos sakamakon tashin hankalin da aka samu yammacin jiya wanda ya haifar da kone kone da kuma harbe harben bindiga.

Talla

Wannan ya biyo bayan abinda ake dangantawa da yunkurin daukar fansa da wasu matasa suka yi sakamakon harin da aka kai karamar hukumar Bassa da ake zargin makiyaya akan Yan kabilar Irigwe abinda yayi sanadiyar rasa rayuka da kuma kona gidaje.

Wasu daga yankunan najeriya da aka dawo da tsaro da zaman lafiya
Wasu daga yankunan najeriya da aka dawo da tsaro da zaman lafiya Kola Sulaimon AFP/File

Harin na zuwa ne kwanakin bayan wani irin sa da aka kai karamar hukumar Riyom abinda ya sa majalisar tsaron jihar ta gudanar da taron gaggawa inda aka baiwa sojoji umurnin kara yawan jami’an su a yankunan kananan hukumomin da ake samun tashin hankalin.

Sanarwar da Daraktan yada labaran gwamnatin jihar Dr Makut Simon Macham ya rabawa manema labarai ta tabbatar da tura jami’an tsaron da kuma kwantar da tarzomar.

Macham yace matakin ya biyo bayan harin da aka kaiwa wasu motoci guda biyu da kuma cinna musu wuta lokacin da matasa suka tare babbar hanyar Gada Biyu.

Gwamnatin Jihar ta gargadi jama’ar jihar da su kaucewa daukar doka a hannun su wajen tare hanya suna kai hari akan matafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI