Najeriya-Zamfara

Kwalara ta kashe mutane 30 a Zamfara

cutar Cholera ta shiga wasu jihohin Najeriya.
cutar Cholera ta shiga wasu jihohin Najeriya. NAN

Hukumomin Jihar Zamfara dake Najeriya sun ce akalla mutane 30 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar kwalara ko kuma amai da gudawa, yayin da ma’aikatar lafiya ta ce mutane da suka harbu da cutar sun kai 2,600.

Talla

Rahotanni sun ce jami’an kungiyar agaji ta MSF tare da hukumomin lafiyar jihar na can suna kula da masu fama da cutar a kananan hukumomin Bakura da Bungudu da Tsafe da Gusau da Zurmi da Kauran Namoda da kuma Birnin Magaji.

Wannan adadi na zuwa ne kasa da sa’oi 24 bayan gwamnatin Jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar mutane 23 sakamakon kamuwa da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.