Zamfara-'Yan bindiga

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaron Najeriya 12 a Zamfara

Rahotanni daga Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun hallaka jami’an tsaron kasar 12 a wani farmaki kan sansanin Sojin kasar da ke jihar Zamfara a yankin arewa maso yammacin kasar.

Wasu Sojin Najeriya.
Wasu Sojin Najeriya. AFP - AUDU MARTE
Talla

Wasu majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun koma kona wasu gine-ginen Sojin baya ga sace tarin makamai.

Har zuwa yanzu dai babu cikakken bayani wadanda suka kaddamar da farmakin, wanda bayanai ke cewa ya faru a Mutumji cikin ranakun karshen mako.

Har yanzu Sojin Najeriyar na ci gaba da fatattakar maboyar ‘yan bindigar jihar ta Zamfara matakin da ke zuwa bayan katse layukan sadarwa don magance matsalar da ta addabi jihar da makwabtanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI