Najeriya-Zamfara

'Yan bindiga sun saki daliban da suka sace a Maradun bayan kwanaki 11

Bello-Matawalle, gwamnan jihar Zamfara.
Bello-Matawalle, gwamnan jihar Zamfara. © Premiumtimes

Gwamnatin jihar Zamfara a tarayyar Najeriya ta bayyana kubutar da dalibai 75 da aka yi garkuwa da su a makarantar gwamnati ta jeka ka dawo da ke garin kaya a karamar hukumar Maradun bayan sun kwashe kwanaki 11 a hannun 'Yan Bindiga.Gwamna Bello Matawalle ya alakanta nasarar da irin matakan da gwamnatinsa ta dauka wajen yakar ‘yan bindigar.Wakilinmu daga Kaduna Aminu Sani Sado na dauke da rahoto akai.