Najeriya na shirin sake karbo bashin fin dala biliyan 4 a ketare
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi majalisar dattawan kasar ta amince da ciwo karin bashin dala biliyan 4 da kuma euro miliyan 710 daga waje.
Wallafawa ranar:
Kudurin na kunshe ne a cikin wasikar da shugaban ya aike wa shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, wadda kuma aka karanta a zauren majalisar a yau Talata.
Buhari ya ce za a karbo rancen ne daga Bankin Duniya da Hukumar tallafawa ci gaban kasashe ta Faransa da kuma Bankin EXIM da ke Amurka da kuma Asusun Tallafawa Noma na Duniya IFAD.
Shugaban Najeriyar ya ce rancen zai bai wa Gwamnatinsa damar aiwatar da muhimman ayyukan raya kasa a sassa daban-daban.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu