Najeriya

Dimokaradiyya: Buhari ya ce gwamnatinsa ta fi sauran gwamnatoci tabukawa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari © Nigeria presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce tun da aka dawo da mulkin dimokaradiyya a shekarar 1999, babu gwamnatin za ta kwatanta kanta da tasa a wajen dawo da Najeriya hayyacinta.

Talla

Shugaban ya bayyana haka ne a a jawabin da ya gabatar a ranar tunawa da samun yancin kan kasar.

Tsohon shugaba kasar, Olusegun Obasanjo ne ya fara mulki tun da dimokaradiyya ta dawo a shekarar 1999, kana ya mika wa Umaru Musa yaradua a shekarar 2007.

Yar’adua bai karasa wa’adin mulkinsa ba sakamakon rashin lafiya, kuma bayan ya mutu a shekarar 2010 ne Goodluck Jonathan, wanda shine mataimakinsa ya karasa wa’adin mulkin Yaradua, ya kuma dora tasa  a shekarar 2011, har zuwa lokacin da Buhari ya buge shi a shekarar 2015.

A jawabinsa ga l’ummar Najeriya, Buhari ya ce abin takaici ne ganin yadda masu adawa suka gaza fahimtar ci gaban da aka samu a gwamnatinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI