Najeriya

'Yan bindiga sun kashe sojoji 2 tare da jikkata 12 a Neja - Gwamna

Hoton domin misali kan 'yan bindiga.
Hoton domin misali kan 'yan bindiga. © Depositphotos

A Najeriya ‘yan bindiga sun kashe sojoji 2 tare da jikkata wasu 12 a wani harin baya bayan nan kagara, shelkwatar karamar hukumar Rafi ta jihar Neja, kamar yadda gwamnan jihar, Abubakar Bello ya sanar.

Talla

Wata sanarwa da kakakin gwamnatin, Mary Noel- Berje ta fitar ta ce su ma ‘yan bindigar sun ji jiki, sakamakon kashe da dama daga cikinsu.

Gwamnan ya ce ‘yan bindigar sun kutsa cikin fadar sarkin Kagara da zummar sace shi, amma aka yi katari sarkin bay a gari.

Ya ce ‘yan bindiga suna hadin gwiwa da ‘yan ta’adda, duba da yadda suke kara yawa, da kuma yadda suke shirya hare hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI