Najeriya-Kaduna

Al'ummar Kaduna sun kalubalanci matakan gwamnati na yaki da 'yan bindiga

Wani yanki na Jihar Kaduna a Najeriya.
Wani yanki na Jihar Kaduna a Najeriya. AFP PHOTO / MICHAEL SMITH

Al'umma da dama a jihar Kaduna da ke Najeriya na kokawa dangane da matakan da gwamnatin jihar ta dauka na dakile aikin 'Yan ta'adda a  jihar inda su ke ganin cewa matakan sunyi tsauri da yawa, kuma suke bukatar a sassauta. A makon da ya gabata ne dai gwamnatin jihar ta hana hawa babura a fadin jihar har na tsawon watanni uku tare kuma katse layukan sadarwa a wasu sassan jihar. Wakilinmu daga Kaduna Aminu Sani Sado na dauke da rahoto akai.