Zamfara-Katsina

'Yan bindiga sun kashe fararen hula 24 a jihohin Zamfara da Katsina

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost

'Yan bindiga a Najeriya sun hallaka akalla mutane 24 a wasu jerin hare hare da suka kai Jihohin Zamfara da Katsina dake fama da matsalar tsaro.

Talla

Rahotanni sun ce a ranar talata 'yan bindigar sama da 100 akan babura sun yi wa kauyen Kuryan Madaro kawanya, inda suka kashe mutane da dama tare da kwace wayoyi da kudaden su.

Kakakin 'yan sandar Jihar Katsina Gambo Isah ya ce wasu 'yan bindigar sun kai hari kauyen Yasore da ke Batsari inda suka hallaka mutane.

Jihohin Zamfara da Katsina na daga cikin yankunan da 'yan bindiga suka fi kai munanan hare hare a yankin arewa maso yammacin Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI