Jama'a zasu soma amfani da kungiyoyin 'yan banga don kare kai da kai

Wasu 'Yan Sa-kai dake yakar ta'addanci a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Wasu 'Yan Sa-kai dake yakar ta'addanci a yankin arewa maso gabashin Najeriya. © Reuters/Akintunde Akinleye

A Najeria, tarin kalubalen tsaron da kasar ke fuskata ta fannin sata da garkuwa da mutane da aika-aikar ‘yan bindiga, yanzu haka sun tilasta wa al’umma a birane da kauyuka daukar zabin yin amfani da kungiyoyin ‘yan banga domin tabbatar da tsaro a unguwanninsu.Sai dai kuma  kamar yadda z aku ji a wannan rahoton na Shehu Saulawa, wani bincike na tabbatar da cewa yawaitar wadannan kungiyoyin na sintiri, na haddasa matsaloli a bangaren na tsaro.