Najeriya - NUPENG

NUPENG ta soke shiga yajin aiki domin tattaunawa da gwamnati

Wani gidan man Najeriya da yayi ambaliya a yankin Neja Delta 18/06/17.
Wani gidan man Najeriya da yayi ambaliya a yankin Neja Delta 18/06/17. REUTERS - Stringer .

Kungiyar Direbobin tankar dakon mai a Najeriya ta soke yajin aikin da ta shirya farawa ranar Litinin saboda lalacewar hanyoyin kasar wanda ke kaiga asarar rayukan ma’aikatan su.

Talla

Shugaban kungiyar reshen kudu maso yammacin kasar Tayo Ayebi ya sanar da sabon matakin, inda yace sun yanke hukuncin janye yajin ne domin tattaunawa da gwamnati.

Yajin aiki

Tun da fari shugaban Yankin Kudu maso Yammacin Najeriya na kungiyar ta NUPENG Tayo Aboyeji ya bayyana shirin, inda yake cewa kungiyar su tayi asarar direbobi da dama tare da kadarori sakamakon lalacewar hanyoyi, inda  yace yajin aikin zai shafi kasa ne baki daya.

Jami’in yace sun dade suna bayyana shirin yajin aikin, amma suke dakatarwa saboda tunanin irin illar da zai haifarwa jama’a ‘yan kasa.

"Abin kunya ga Najeriya"

Shugaban kungiyar yace a halin da ake ciki yanzu, tankin mai kan kwashe kwanaki 5 zuwa 6 idan yayi dakon man daga Lagos zuwa Abuja saboda tabarbarewar hanyoyin, wanda ya bayyana shi a matsayin abin kunya ga Najeriya.

Aboyeji yace kokarin su na janyo hankalin hukumomin Najeriya akan lalacewar hanyoyin yaci tura.

‘Yan Najeriya sun dade suna korafi dangane da lalacewar hanyoyin motocin kasar, inda suke zargin gwamnati da rashin kula saboda yadda jami’an ta ke zirga zirga ta jiragen sama, yayin da talakawa ke shan ukuba.

Lalacewar hanyoyin na daya daga cikin abinda barayi da ‘Yan bindiga ke amfani da shi suna yiwa mutane fashi da kuma garkuwa da jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI