'Yan bindiga-Najeriya

Mutane 15 sun tsere daga hannun masu garkuwa a jihar Borno

Matsalar garkuwa da mutane don neman fansa ya zama ruwan dare a kusan dukkanin jihohin arewacin Najeriya.
Matsalar garkuwa da mutane don neman fansa ya zama ruwan dare a kusan dukkanin jihohin arewacin Najeriya. REUTERS - AFOLABI SOTUNDE

Rahotanni daga Najeriya sun ce akalla mutane 15 suka tsere daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su a Jihar Borno, bayan sun kwashe kwanaki 6 suna gudu a daji.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce an kama wadannan mutane ne a hare hare daban daban da 'yan bindigar suka kai kauyen Takulashi da ke Yankin Chibok a Jihar Borno da kuma Kufre da ke Jihar Adamawa.

Kwamishiniyar kula da harkokin mata a Jihar Borno Zuwaira Gambo ta yabawa jajircewar mutanen da suka hada da mata 6 da yara 9.

Kwamishiniyar matan Zuwaira Gambo ta kara da cewa cikin mutanen da suka tsere daga hannun masu garkuwar har da wata mata mai cikin watanni 8 da ta yi tafiyar kwanaki 6 a kasa daga dajin Buni Yadi da ke gab da jihar Yobe zuwa Damboa a jihar Borno tafiyar da ke da nisan kilomita 90 kuma a kasa.

Bayanai sun ce uku daga cikin matan da yaransu 6 ‘yan bindigar sun yi garkuwa da su ne yayin wani sumame a Takulashi cikin watan Oktoban bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI