Najeriya-Zabe

Majalisar dattijan Najeriya ta goyi bayan tsarin 'yar tinke a zaben fidda gwani

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan
Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan Twitter/Nigerian Senate

A yunkurinta na kawo karshen Siyasar kudi, Murdiya da dauki dora, Majalisar dokokin Najeria ta amince da salon zaben fitar da dan takara ta hanyar bin layi bayan dan takara, wato abinda aka fi sani da suna Kato-bayan-Kato, ko ‘yar tinke, tare da amincewa hukumar zaben kasar ta bayyana sakamakon zabe nan take ta hanyar yanar gizo. Kabir Yusuf na dauke da karashen rahoto.