NAJERIYA-TSARO

Majalisar Zamfara ta dakatar da mambobinta 2 saboda alaka da 'Yan ta'adda

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle © Governor Matawalle

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara da ke Najeriya ta dakatar da mambobin ta guda biyu da ake zargin suna mu’amala da ‘Yan bindigar da suka hana zaman lafiya a jihar.

Talla

‘Yan majalisar sun hada da Yusuf Muhammad Anka dake wakiltar mazabar Anka da Ibrahim Tukur Bakura dake wakiltar mazabar Bakura.

Daraktan hulda da ‘Yan Jaridu na Majalisar Mustapha Jaafaru Kaura yace ‘Yan Majalisun guda biyu zasu kauracewa zaman Majalisar na watanni 3 har zuwa lokacin da za’a kammala bincike akan su.

Yan bindiga a Najeriya
Yan bindiga a Najeriya © Daily Trust

Kaura yace tuni aka baiwa kwamitin da’a na Majalisar umurnin gudanar da bincike akan su tare da hukumomin tsaron jihar kamar yadda zaman Majalisar ya amince.

‘Dan Majalisa Yusuf Alhassan Kanoma ya gabatar da bukatar daukar mataki akan ‘Yan Majalisun guda biyu wadanda yace suna murna lokacin da ‘Yan bindiga suka kama mahaifin shugaban Majalisar Alhaji Muazu Abubakar Magarya.

Kanoma ya kuma zargi ‘Yan Majalisun guda biyu da hannu wajen kashe tsohon ‘dan majalisar dake wakiltar Shinkafi Muhammad G. Ahmad wajen tseguntawa Yan bindiga bayanan tafiyar sa domin hallaka shi.

‘Dan Majalisar dake wakiltar mazabar Birnin Magaji Nura Dahiru Sabon Birni Dan Ali ya goyi bayan kudirin, inda yace duk yunkurin da akayi na kubutar da mahaifin Kakakin Majalisar daga hannun Bello Turji yaci tura.

Tuni Majalisar ta tube mutanen biyu daga shugabancin kwamitocin ta, yayin da aka fara bincike akan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI