Nijar

Soja Zasu Bada Mulki Watan Biyu 2011

rfi

Shugabannin Gwamnatin Mulkin Sojan kasar Nijar sunyi alkawarin mika mulki hannun farar hula cikin watan biyu na shekara ta 2011 kamar yadda gamayyar kungiyoyin kasar suka basu.A watan jiya ne dai Gamayyar Kungiyoyi na siyasa da ‘yan kasuwa suka nemi gwamnatin Mulkin sojan dasu mika mulki ga farar hula nan da watan biyu na badi.Wani mai magana da yawun Gwamnatin Sojan ya fadi cewa sun karbi tsarin da aka mika masu, na mika mulkin, koda shike basufadi takamaiman ranar da zaayi zaben kasar ba.Sojan kasar karkashin Jagorancin Manjo Salou Djibo sun kwace mulki hannun tsohon Shugaba Mamadu Tandja, ranar 18 ga watan biyu inda sukayi alkawarin yin gyaran fuska a kasar da ganin anyi zabe karbabba.Kasar Nijar wadda take cikin kasashe da ake fama da talauci, ayanzu haka ana fama da matsalar yunwa, kamar yadda majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar.