Kalla Hankurau Minista a fadar shugaban Jamhuriyar Nijar

Sauti 04:58
Tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou a lokacin da ya ke ganawa da shugaban Faransa Francois Hollande
Tsohon shugaban Jamhuriyar Nijar, Mahamadou Issoufou a lokacin da ya ke ganawa da shugaban Faransa Francois Hollande Reuters/John Schults

Gwamnatin kasar Nijar ta samu sama da kudaden tallafin da ta nema daga masu hannu da shuni na duniya sakamakon zaman taron da suka gudanar a birnin Paris na kasar Fransa, domin neman kudaden da za ta cike gibin aikin bunkasa tattalin arziki da ci gaban rayuwar al’ummarta a cikin shekaru hudu masu zuwa. Kalla Hankurau minista ne a fadar shugaban kasar Jamhuriyar Nijar, ya ce an samu sama da kudaden da suka nema da farko.