Majalisar Nijar ta yi zama na musamman game da Kokuwa

Sauti 10:01
Filin wasan kokuwar gargajiya da aka gudanar a Maradi Nijar
Filin wasan kokuwar gargajiya da aka gudanar a Maradi Nijar Awwal Janyau RFI Hausa

Bayan samun sabani da rikici a kokuwar gargajiya da aka gudanar a bana a birnin Yamai Jamhuriyyar Nijar, Majalisar dokokin kasar ta yi wani zama na musamman tare da Ministan Wasanni Kunu Hassan domin jin bahasin dalilan da suka haifar da rikici a kokuwar. A cikin shirin Duniyar wasannin mun ji irin matakai da aka dauka domin kaucewa matsaloli da tashin hankalin da suka faru baya.