Nijar

An kai harin bom da bindiga a gidan yarin birnin Yamai na Nijar

Wasu sojojin kasar Nijar
Wasu sojojin kasar Nijar RFI / Sonia Rolley

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar, sun ce an dauki dagon lokaci ana jin karar harbe-harbe a cikin gidan yarin birnin Yamai, fadar gwamantin kasar, a yau din nan.Lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen da kawo yanzu ba a kai ga tantance adadinsu ba.Shaidu a birnin na Yamai sun ce an soma jin karar harbe harben ne da misalin karfe uku na ranar yau, kuma bisa ga dukkan alamu wasu fursunoni ne suka karbe makamai daga hannun jami’an tsaron gidan yarin, wanda ke tsakiyar birnin na Yamai, inda suka afka wa jami’an dake gadin gidan.Kawo yanzu dai, ba wasu cikakkun bayanai a game da hakikannin wadanda suka kai wannan hari, yayin da aka tura dimbin jami’an tsaro domin yi wa gidan yarin kawanya.Wannan lamari dai yana faruwa ne mako daya bayan da wasu ‘yan kunar bakin wake, suka kai hare-hare a wani barikin soja da ke garin Agadez da kuma cibiyar kamfanin hako makamashin Uranium na Areva, mallakin kasashen Faransa da kuma Nijar a garin Arlit da ke Arewacin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da 30 cikinsu kuwa har da sojoji akalla 20.Ministan Shari'a, kuma kakakin gwamnatin ta Niger, Maru Amadu ya tabbatar da harin, inda ya ce wasu daga waje ne suka kai.ministan ya kuma tattabatar da mutuwar akalla mutane 2.