Faransa-Nijar

Faransa tace ba kwabon da aka biya wajen kubutar da Faransawa

Shugaban Faransa François Hollande tare da Faransawan da aka sace a Nijar a lokacin da suk isa Birnin Paris bayan kubutar da su
Shugaban Faransa François Hollande tare da Faransawan da aka sace a Nijar a lokacin da suk isa Birnin Paris bayan kubutar da su REUTERS/Jacky Naegelen

Gwamnatin Kasar Fraansa tace babu ko kwabon da aka biya wajen ganin an sako Faransawan da aka sace a Jamhuriyar Nijar, yayin da kafofin yada labaran Faransa ke cewa an biya makudan kudaden da suka kai tsakanin euro Miliyan 20 zuwa 25 kafin a sako su.

Talla

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande, wanda ke jawabi jim kadan bayan da Faransawan da aka sace a Jamhuriyar Nijar suka isa Faransa a jiya Laraba, ya ce babban abinda ke gaban kasar shi ne kokarin ‘yantar da wasu Faransawa guda Bakwai da ake yi garkuwa da su a sassa daban daban na duniya.

Bisa ga al’ada hukumomin Faransa kan ce sam ba su biyan kudin fansa domin kwato ‘yan kasar da wasu kungiyoyi suka yi garkuwa da su sai dai wasu majiyoyi a kusa da wadanda suka taka rawa wajen ‘yantar da wadannan mutane sun ce an biya fansar Euro Milyan 20 zuwa 25 domin ‘yantar da su.

Ministan tsaron Faransa Jean-Yves Le Drian, ya karyata zargin yana mai cewa kasar ba ta biya ko sisin kwabo ba.

‘Babu farmaki ballatana samame a kan wadanda ke garkuwa da mutane wai domin kwato su’, inji Le Drian.

Wani babban jami’in tsaro a kasar Nijar, ya ce an dauko mutanen 4 ne daga yanki Anefis a arewa maso gabacin kasar Mali, yankin da tun kafin soma bayyana ayyukan ta’addanci na wannan zamani ake da kungiyoyin ‘yan bindaga da suka yi kaurin suna wajen sace mutane da kuma yin garkuwa da su har sai an biya fansa.

A cikin wannan yanki da ya hada kasashen Nijar, Mali, Aljeria da kuma Mauritaniya, da akwai wasu mutane cikinsu har da shugabannin al’ummomi ne da suka shahara wajen ceto wadanda ake garkuwa da su, inda su ma ake biyansu makuddan kudade a matsayin ladar aikinsu.

Amma a daya bangaren, wata majiya da ke da masaniya dangane da yadda aka ‘yantar da wadannan mutane, ta ce an ‘yantar da su ne bisa sharadin cewa, ba a za a tuhumi shugaban kungiyar Ansaruddin ba Iyag Agali a gaban kotu.

Aghali, wanda a cikin shekarun 1990 wanda ya taba jagorantar wata kungiyar ‘yan tawayen Azibinawa a kasar Mali, na daga cikin wadanda gwamnatin Mali da kuma kasashen Yamma ke zargi da ayyukan ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.