Nijar

Maradi: ‘Yan kasuwa suna kuka da tsadar haya

Harabar wasu shahunan 'Yan kasuwa a Maradi
Harabar wasu shahunan 'Yan kasuwa a Maradi wikimedia

‘Yan kasuwa a birnin Maradi na Jamhuriyar Nijar suna kuka da tsadar kudaden haya da ma’aikatar magajin gari ta kayyade ga sabbin shaguna a cikin sabuwar kasuwar garin ta Maradi. Kudaden da suka ce abin ya wuce kima kuma ba a yi masu adalci ba sai dai hukumomin Ofishin Magajin garin na cewar sun yi hakan ne saboda kula da kasuwar. Wakilinmu Salisu Issa ya duba wannan dambarwa a cikin Rahoton da ya aiko.

Talla

Rahoto: Maradi: ‘Yan kasuwa suna kuka da tsadar haya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.