Niger

Koyon faransanci a CCFN Damagaram

Centre Culturel Franco-Nigerien
Centre Culturel Franco-Nigerien CCFN

'Yan Najeriya da dama ne ke samun horo karkashin wata hulda da ta hada jami'o'in kasar da kuma Cibiyar Yada Al'adun Faransa da Nijar CCFN da ke birnin Damagaram Zinder.Wasu daga cikin manyan makarantun Najeriya da ke aikewa da dalibansu zuwa wannan cibiya sun hada da jami'ar Bayero da ke Kano da kuma kwalejin ilmi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, kuma a wannan mako ne aka gudanar da bikin yaye wasu dalibai da suka samu horo a cibiyar kamar yadda wakilinmu Ibrahimm Malam Tchillo ke cewa a wannan rahoto.