Turai

Turai zata hada kai da Musulmi domin yakar ta’addanci

Jami'an tsaron kasar Belgium a birnin Brussels
Jami'an tsaron kasar Belgium a birnin Brussels REUTERS/Stringer

Kungiyar Kasashen Turai na shirin kaddamar da wani shirin yaki da ayyukan ta’adanci tare da hadin kan kasashen Musulmi. ta hanyar musayar bayannan sirri a tsakaninsu, bayan hare haren da aka kai a kasashen Faransa da Belgium.

Talla

A wani mataki na fito da dabarun zakulo masu kai hare-haren ta’addanci a kasashen Turai, Ministocin kungiyar kasashen na Turai sun amince da bukatar yin aikin hadin Guiwa a tsakaninsu da kasashen Larabawa, domin kawar da ayyukan ta’addanci.

Bayan kammala wasu batutuwa da aka yi a birnin Brussels tsakaninsu da kasashen na Larabawa, kungiyar Turai ta cim ma matsayar cewar yin hakan zai yi tasiri, musamman wajen wayar da kan juna.

Wannan na zuwa ne a dai dai lokacin da Dubban Mutane suka yi zanga-zanga a Chechnya na kasar Rasha, da kone konen Mujami’u da aka yi a Jamhuriyyar Nijar domin nuna adawa da mujallar Charlie Hebdo da ta ci zarafin musulmi.

Kasashen kungiyar Tarayyar Turai dai na ganin yadda matsalar rashin fahimtar juna da ake samu tsakanin mabiya Addini ke zaman babbar barazana ga sha’anin tsaro a sassan Duniya baki daya.

Daga cikin kasashen Larabawan da aka bayyana sun nuna agoyon baya ga wannan shirin na Kungiyar Tarayyar Turai, sun hada da Turkiya da Masar da Yemen da Algeria da kuma kasashen yankin Gulf.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.