niger-siyasa

Hama Amadu ya ce gobe Assabar zai koma gida a Niger, daga gudun hijira a Faransa

Hama Amadou, a lokacin da yake shugabancin majalisar dokokin  Niger, le 6 novembre 2013 à Niamey.
Hama Amadou, a lokacin da yake shugabancin majalisar dokokin Niger, le 6 novembre 2013 à Niamey. AFP PHOTO / ISSOUF SANOGO

Tsohon shugaban majalisar dokokin kasar Jamhuriyar Nijar Hama Amadou ya ce gobe asabar zai koma gida Niger domin tsayawa takarar nemen shugaban kasar a zaben da za a gudanar a 2016.  

Talla

Hama ya ce, babu wanda ya isa ya hana shi komawa gida, kuma idan akwai wanda zai yi wa bayani bai wuce kotu ba, amma ba gwamnatin Muhammadou Issofou ba.

A baya Hama Amadu dai, ya kasance abokin kawance gwamnatin Mahamadu Isufu ne, kafin su raba gari sakamakon rabon mukaman a gwamnati da ya ce ba a yi wa jam’iyarsa ta FA Lumana Afrika badalci ba.

Ya kuma fice daga kasar ne inda yayi hijira a kasar Faransa, cewa shugaban kasar Mahamadu Isufu na neman kashe shi, bayan da gwamnati ta zarge shi da safarar jarirai 2 da ya dauka reno daga tarayyar Najeria ba bisa kan ka’ida ba, zargin da har kulum yake musuntawa da cewa ‘ya ‘yansa ne
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI