Nijar
Sana'ar kankara a lokacin zafi a Nijar
Wallafawa ranar:
A Jamhuriyar Nijar, yayin da ake fuskantar tsananin zafi a wannan lokaci da ya kai maki 46 a yawancin yankunan kasar, Masu hada hadar kankara ko Glace da faransanci sun bude wata kasuwa a jihar Maradi, inda daruruwan masu saida kankarar ke haduwa da zaran anyi sallar magaruba har zuwa tsakiyar dareWakilin mu a Maradi Salissou Issa ya hada mana rahoto.