Niger

Yara sama da dubu biyar sinadarin Flour ya yiwa illa a Nijar

AFP PHOTO / Mustafa Ozer

Yara sama da dubu biyar ne ruwan sha dake kumshe da sinadarin Fluor ya nakasa a garin Tsibiri na Jihar Maradi tun shekara ta 2000, daga cikinsu yara 271 sun samu nakasa ta rashin hannuwa da kafuwa, sannan ga manyan kawuna yayin da hakorinsu sukayi baki tik.

Talla

Wannan ne ya sa iyayen yaran tare da tallafin kungiyar kare hakkin dan Adam ta ANDDH suka shigar da kara don samarwa wadannan yaran diyya da za ta sa su samu saukin rayuwa, to sai dai duk da an ce gwamnati ce ke da wannan laifi kumaya kamata ta biya kowane yaro Cfa miliyon 10 a matsayin diyya, har yanzu shiru.

Salisu Isah na dauke da rahoro daga maradi

Yara sama da 200,000 sinadarin Flour ya yiwa illa a Niger

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.