Itacen Dakwara na yaki da kwararowar hamada

Sauti 20:02
Yankin Bosso dake Nijar
Yankin Bosso dake Nijar ISSOUF SANOGO / AFP

Shirin Muhallinka Rayuwarka ya mayar da hankali ne a Jamhuriyyar Nijar game da muhimmacin iccen Dakwara wajen kare gurgusowar Hamada da kuma wasu alfanun iccen ga kasar noma.

Talla

Daya daga abinda ke kare hamada ta hanyar rage gusowar rairai tare da iska sannan da raya kasar noman da ta sallace, Masana na ganin babu kamar iccen Dakwara wanda ke fitar da Karo.

Tun shekara ta 2003 gwamnatin shugaba Tandja Mahamadu ta fito da wani sabon tsari na bunkasa noma wannan icce a fadin kasar.

Wannan kuma don yaki da gurgusowar hamada sannan da samar da kudin shiga ga manoma lura da irin makudan kudaden karo da manoman kasashen Sudan da Tchadi ke samu, abin da ya sa suka fita sha’anin noma suka mayar da hankali ga iccen na dakwara.

Sai dai shekaru 13 bayan wannan hobbasa da dama daga manoman Dakwara sun yi watsi da wannan sana’a saboda rashin samun biyan bukata bayan sun shuka ekoki da Dama.

Shirin ya tattauna da manoman Iccen da kuma masana kan yadda za a farfado da noman shi da kuma matakan samuun Karo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI