Nijar

Sojojin Jamhuriyar Nijar 14 sun rasa rayukansu

Rundunar sojin Nijar ta ce sojojinta 14 ne suka rasa rayukansu, 29 suka samu raunuka, yayinda suka samu nasarar kasha da dama daga cikin mayakan boko Haram daga watan Yuli zuwa ranar ashirin ga watan Satumban da ya gabata.

Talla

Kakakin ma’aikatan tsaron Nijar Kanal Moustafa Ledru yace baya ga samun nasarar kashe mayakan Boko Haram 123, rundunar sojin kasar ta kwace tarin makamai daga hannun mayakan.

Kanal Ledru ya ce kawo yanzu, an kwace yankuna hudu daga hannun mayakan na Boko Haram, wadanda a da suka mamaye a da, kan iyakar kasar da Najeriya.

Jihar Diffa da ke kan iyakar Nijar da Najeriya ta fara fuskantar hare-haren Boko Haram a watan Fabarairun shekara ta 2015.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.