Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Intinikar Alhassan kan dage zaben Nijar

Sauti 03:06
Daya daga cikin jami'an gudanar da zabe a Nijar
Daya daga cikin jami'an gudanar da zabe a Nijar ISSOUF SANOGO / AFP
Da: Abdurrahman Gambo Ahmad
Minti 4

A taron da suka gudanar jiyar talata a birnin Yamai, jam’iyyun siyasar jamhuriyar Nijar sun amince a sake dage zaben kananan hukumomin kasar wanda ya kamata a yi ranar 8 ga watan janairu mai zuwa. Wasu daga cikin dalilai dangane da haka sun hada da bai wa hukumar zabe damar shirya rajista irin ta zamani da ake kira Biometric da kuma bai wa sauran jam’iyyun damar kintsawa zaben. To sai dai jam’iyyun adawa da kuma na ‘yan ba ruwanmu sun kaurace wa wannan taro na jiya. Akan wannan ne Nura Ado Suleiman ya tattauna da Intinikar Alhassan kakakin jam’iyyun adawa na Jamhuriyyar Nijar.   

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.