Isa ga babban shafi
Nijar

Jam’iyyun adawa sun nuna fushinsu kan dage zabe a Nijar

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou.
Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou. AFP PHOTO / FAROUK BATICHE
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
Minti 1

Jam’iyyun adawa a Jamhuriyar Nijar sun nuna fushinsu dangane da dage zaben kananan hukumomin kasar da ya kamata a yi ranar 8 ga watan janairu mai zuwa, inda suke zargin gwamnatin da shirya wata makarkashiya.

Talla

A cewar kakakkin Jam’iyyar kasar dage Mulki Asumana Muhamadu, an dage zaben ne domin bai wa hukumar zabe damar shirya rejista irin ta zamani da ake kira Biometric, da kuma bai wa sauran jam’iyyun damar kintsawa zaben.

To sai dai jam’iyyun adawa da kuma na ‘yan ba ruwanmu sun nuna shaku dangane da dalilan da aka bayar.

Dage zaben ya biyo bayan taron da aka gudanar ranar talata a birnin Yamai, da ya amince a sake dage zaben kananan hukumomin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.