Nijar

An hana fararen hula gudanar da zanga-zanga

An hana fararen hula gudanar da zanga-zanga a Nijar.
An hana fararen hula gudanar da zanga-zanga a Nijar. AFP PHOTO / BOUREIMA HAMA

A wannan juma’a ne kungiyoyin fararen hula a Jamhurriyar Nijar suka shirya zanga zanga, to sai dai hukumomi a birnin Yamai sun haramta gudanar da wannan gangamin saboda dalilai na tsaro.

Talla

A cikin watan disambar da ya gabata ne dai kungiyoyin na fararen hula da kuma ‘yan adawa suka gudanar da zanga-zangar farko inda suke zargin gwamanati da rashawa, yayin da magoya bayan gwamnati suka gudanar da tasu zanga-zanga domin jaddada goyon bayansu ga shugaban kasar Issoufou Mahamadou a karshen makon da ya gabata.

Kungiyoyin fararen hular dai sun bayyana cewa sun yi matukar mamaki dangane da wannan mataki domin kuwa ba su da niyyar tayar da hankulan jama’a domin kuwa zanga-zanga ce ta ruwan sanyi.

Wasu dai na zargin gwamnati da yin amfani da siyasa domin hana wannan gangami, Yanzu haka dai shugabannin Kungiyoyin fararen hular sun ce suna nazari dangane da irin matakan da za su dauka dangane da wannan mataki.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI