Nijar-Diffa

Mayakan Boko Haram sun kai harin bazata a yankin Diffa

Taswirar da ke nuna yankin Diffa
Taswirar da ke nuna yankin Diffa

Mayakan Boko Haram sun kai wani harin bazata kan wani barikin sojin Nijar da ke kudu maso gabashin kasar.

Talla

Jami’ai sun ce yayin harin da mayakan na Boko Haram suka kai, kan barikin sojin da ke Geskerou a yankin Diffa, sojin Nijar guda biyu sun rasa ransu, yayinda mayakan suka kona motocin soji guda uku.

To sai dai Sojin Nijar sun maida martani ta hanyar yiwa mayakan luguden wuta da jiragen yaki, inda suka samu nasarar kashe da yawa daga cikinsu, sauran kuma suka tsere.

A watan da ya gabata ne, gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta sanar da cewa akalla mayakan Boko Haram 50 suka mika makamansu, 31 daga ciki kuma sun yi hakan ne a yankin Diffa.

A satin da ya gabata kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya ce nan bada dadewa ba, zai tura tawagarsa kai ziyara zuwa Najeriya, Kamaru da kuma kasar Chadi, dangane da halin da ake ciki na yaki da ta’addanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.