An kafa dokar ta baci a yankuna bakwai na Nijar
Wallafawa ranar:
Kasar Nijar ta ayyana dokar ta baci a wasu yankunan yammacin kasar dake makwabtaka da kasar Mali sakamakon hare-haren ta'addanci da masu jihadi ke ta kaiwa.
Wata sanarwan Gwamnati tun jiya Jumaa na cewa kafa dokar ta bacin ya shafi wurare 7 a yankunan Tilaberi da Tahoua.
Yanzu ke nan an karawa jami'an tsaro karfin guiwa da izinin binciken dukkan inda suke zargin akwai alamun rashin gaskiya.
A cewar sanarwan yawaitan hare-hare da ake kaiwa a yankunan na da hatsarin gaske ga mazauna yankunan.
Sauran sassan sun hada da Ouallam, Ayorou, Bankilare, Abala da Banbangou a yankin Tilaberi, sai kuma Tassara da Tilla a yankin Tahoua.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu