Bakonmu a Yau

Gwamnatin Nijar ta shigar da karar kamfanin Areva

Sauti 03:34
Wani sashi na kamfanin hakar ma'adanai na Areva da ke kasar, Faransa da aka dauka a ranar 7 ga watan Janairun da ya gabata.
Wani sashi na kamfanin hakar ma'adanai na Areva da ke kasar, Faransa da aka dauka a ranar 7 ga watan Janairun da ya gabata. REUTERS/Robert Pratta/File Photo

Gwamnatin Nijar ta shigar da kamfanonin Somair da kuma Cominack kara, sakamakon yadda kamfanonin biyu suka share tsawon shekaru biyu ba sa biyan haraji ga kananan hukumomin da suke gudanar da ayyukansu na hako ma’adinai. Kamfanonin wadanda ke a matsayin rassan kamfanin Uranium na Areva mallakin Faransa, sun ce sun dakatar da biyan kudaden harajin ne, sakamakon wata yarjejeniya da ke tsakaninsu da gwmnatin Nijar, ikirarin da gwamnatin ta musanta. Abdourahman Moli shi ne magajin garin Arlit, daya daga cikin gundumomi 15 da lamarin ya shafa, ya ce za su tashi tsaye domin kwato hakkokinsu daga wadannan kamfanoni da ke gurbata ma su muhalli da ma haddasa cucutuka.