An sake bude jami’ar Yamai a yau Lahadi
Wallafawa ranar:
Mako daya bayan rufe jami'ar Yamai dake Jamhuriyar Nijar, saboda boren dalibai, gwamnatin kasar ta sake bude jami'ar a yau Lahadi biyo bayan koken jama’a.
Ministan Ilimi Muhammad Bin Oumar ya fadi cikin wata sanarwa cewa matakin sake bude Jami'ar na zuwa ne saboda koke daga jama’ar dake bukatar a sake bude Jami’ar.
Sanarwar na cewa Shugaban kasar Mahammadu Issoufou ya gana da kungiyoyin daliban Jami’ar domin yi musu hudubar tattalin zaman lafiya.
A halin da ake ciki rundunar ‘yan sandan kasar ta ce ana tsare da dalibai uku wadanda ake zargin suna da hannu a rikicin da ya haddasa mutuwar dalibi daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu