Nijar

Issoufou Alfaga na Nijar ya lashe gasar Taekwondo ta duniya

Dan Nijar Issoufou Alfaga Abdoulrazak zakaran Taekwondo na duniya
Dan Nijar Issoufou Alfaga Abdoulrazak zakaran Taekwondo na duniya REUTERS/Issei Kato

Issoufou Alfaga Abdoulrazak na kasar Nijar ya lashe zinari a gasar Taekwondo ta duniya da aka gudanar a Koriya ta Kudu. Alfaga ya lashe zinarin ne bayan ya doke dan wasan Birtaniya Mahama Cho.

Talla

Alfaga ya samu nasarar ne bayan ya doke dan wasan Mali a zagayen farko, ya doke na Faransa a zagaye na biyu, sannan ya doke dan wasan Brazil a zagayen na uku.

A zagayen dab da na karshe ya doke dan wasan Gabon ne Anthony Aubame, sannan ya zo ya doke Mahama na Birtaniya a wasan karshe.

A bara Alfaga ya lashe wa Nijar azurfa a Taekwando inda ya zo matsayi na biyu a wasannin Olympics da aka gudanar a Brazil.

Shi ne dan wasa na biyu da ya lashewa Nijar kyauta a wasannin Olympics bayan dan dambe Issaka Dabore da ya lashe tagulla a 1972 a Munich.

Yanzu za a zira ido a ga rawar da Alfaga zai taka a wasannin Olympics da za a gudanar a Tokyo a shekarar 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.