Nijar

Yan Boko haram sun kai hari a wani kauyen Diffa

Gwamnan Diffa Laouali Dan Dano da tawagarsa
Gwamnan Diffa Laouali Dan Dano da tawagarsa

Mayakan kungiyar boko haram sun yi garkuwa da mata 37 tare da kashe mutane 9 a wani harin da suka kai a ranar lahadin da ta gabata a wani kauye Ngalewa a jihar Diffa dake kudu maso gabashin jamhuriyar Niger . 

Talla

A watan janairu shekarar bana duk da matakan tsaro  mayakan na Boko Haram sun kai hari  kan barikin sojin da ke Geskerou a yankin Diffa, sojin Nijar guda biyu sun rasa ransu, yayinda mayakan suka kona motocin soji guda uku.

To sai dai Sojin Nijar sun maida martani ta hanyar yiwa mayakan luguden wuta da jiragen yaki, inda suka samu nasarar kashe da yawa daga cikinsu, sauran kuma suka tsere.

 Gwamnan jihar Diffa Laouali Dan Dano da tawagarsa  sun samu isa yankin da yan kungiyar boko suka kai harin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.