Nijar

Cutar hanta ta kashe mutane 38 a Nijar

Samar da magunguna kyauta na daga cikin matakan da gwamnatin Nijar ke dauka na yaki da cutar hanta da ta kashe mutane 38
Samar da magunguna kyauta na daga cikin matakan da gwamnatin Nijar ke dauka na yaki da cutar hanta da ta kashe mutane 38

Ofishin jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, mutane 38 suka mutu a yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar sakamakon kamuwa da cutar hanta da ake kira da Hepatitis E a harshen Turanci.

Talla

Sanarwar da ofishin ya bayar, ta nuna cewar mutane dubu 1 da 446 suka kamu da cutar a yankin daga watan Janairu zuwa Yuli na wannan shekarar, kuma tuni 38 sun rasa rayukansu.

Sai dai a zantawarsa da sashen hausa na RFI, Ministan Lafiya na Nijar, Dr. Iliya Mainasara da ya tabbatar da mutuwar mutanen ya ce, suna daukan matakai don ganin cewa sun magance yaduwar cutar.

Samar da magunguna kyauta da kuma wayar da kan al’umma kan kauce wa kamuwa da cutar na cikin matakan da gwamnatin Nijar ke dauka kamar yadda Dr. Mainasara ya bayyana.

Ministan ya kara da cewa, a halin yanzu an samu sassaucin yaduwar cutar sakamakon matakan da aka dauka na yaki da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.