Bakonmu a Yau

Mahamman Kaka Tuda kan shirin yi wa mayakan Boko Haram afuwa

Sauti 03:13
Jihar Tillabery da ke Jamhuriyar Nijar
Jihar Tillabery da ke Jamhuriyar Nijar RFI/Sayouba Traoré

Gwmanatin Jamhuriyar Nijar, ta bai wa ‘yan Boko Haram nan zuwa ranar 31 ga watan Disamba mai zuwa, domin ajiye makamansu, wanda hakan zai ba su damar cin moriyar shirin yafiya da kuma ba su horo kan yadda za su cigaba da rayuwa a cikin al’umma. A lokacin da ya ziyarci wani sansani da aka tattara ‘yan Boko Haram 160 da suka ajiye makamansu, gwamnan jihar Diffa Mahammadou Lawaly Dan Dano, ya ce ba za’a amince da wanda ya wuce wannan lokaci ba tare da ya ajiye makaminsa ba. Mahamman Kaka Tuda, shi ne shugaban ofishin cibiyar kare hakkin bil’adama ta Alternative reshen Diffa, ya bayyana wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal yadda yake kallon wannan shiri.