Ministan lafiya na Nijar kan dalilan da ya su rufe Asibitoci masu zaman kansu da shagunan saida magunguna 14

Sauti 03:39
Wasu magungunan jabu da hukumomin kasar Senegal suka kwace.
Wasu magungunan jabu da hukumomin kasar Senegal suka kwace. REUTERS/Pape Demba

Gwamnatin Nijar ta bayar da umurnin rufe asibitoci da kuma gidajen sayar da magunguna masu zaman kansu guda 14 a kasar, tare da bai wa wasu 24 takardar gargadi saboda kauce wa ka’ida a cikin ayyukansu. Ministan kiwon lafiya na kasar Dr Iliyassou Idi Mainassara, ya ce an dauki matakin ne bayan da bincike ya tabbatar da cewa asibitocin da kuma gidajen sayar da magungunan sun daina mutunta ka’ida. AbdoulKareem Ibrahim Shikal ya tattauna da Ministan kan wannan al'amari.