Nijar

Nijar zata farfado da shirin shimfida bututun mai zuwa Kamaru

Za'a cigaba da nazarin shimfida bututun mai daga Nijar zuwa Kamaru
Za'a cigaba da nazarin shimfida bututun mai daga Nijar zuwa Kamaru businessincameroon.com

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar, ta ce a cikin shekara mai zuwa za ta ci gaba da tattaunawa da kasashen Chadi da Kamaru, domin shimfida jerin bututun man fetur da zai tashi daga kasar; arewacin jihar Diffa zuwa tashar ruwan Kribi da ke Kamaru.

Talla

Yayin da yake karin haske kan shirin, Ministan kudin Nijar Hassoumi Massaoudou, ya ce tattaunawar zata kuma duba yi wuwar karkata akalar shinfida bututun man zuwa tshar ruwa dake birnin Kwatano idan aka cigaba da fuskantar barazanar tsaro daga mayakan Boko Haram a Kamaru.

Tun shekara ta 2013 ne ake tattaunawa kan wannan shiri, sai dai bullar ‘yan Boko Haram ya haifar da cikas.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.