Nijar

Nijar ta kama tan 13 na magungunan jabu a Yamai

Rundunar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijar ta kama sama da tan 13 na magunguna jabu da aka yi safarar su cikin kasar
Rundunar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijar ta kama sama da tan 13 na magunguna jabu da aka yi safarar su cikin kasar REUTERS/Pape Demba

Rundunar yaki da fataucin miyagun kwayoyi da sauran magunguna na jabu ta Jamhuriyar Nijar ta kama magugunguna marasa kyau da yawansu ya kai ton 13 a birnin Yamai.

Talla

Daga cikin wadanda ke da hannu a wannan fatauci har da kamfanonin da ke da izinin shigo da magunguna a kasar.

A lokacin da ta ke sanar da wannan kame, Keftin Nana Aicha Ousman daya daga cikin manyan jami‘an hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyin, ta ce jami’ansu sun yi nasarar gano wadannan magunguna na jabu ne sakamakon wani samame da suka aiwatar.

Tuni dai aka mika wadannan mutane a hannun ma’aikatar shara’a domin hukunta su, kuma a cewar mataimakin shugaban ofishin mai shigar da kara na gwamnati Maman Tsayyabou Issa, tabbas za a hukunta masu hannu a lamarin don sauran jama’a su dauki darasi musammanwadanda ke da sha’awar shiga irin wannan haramtacciyar harka.

An jima dai masu fafutukar kare hakkin bil’adama na jan hankulan mahukuntan kasar don sanya kafar wando daya da masu irin wannan safara, kuma daya daga cikinsu Dambaji Son Allah, ya ce ya zama wajibi a dauki matakin ba sani ba sabo akan wadannan mutane.

A kwanakin da suka gabata ne ma’aikatar lafiya ta kasar ta rufe wasu asibitoci masu zaman kansu tare da gargadi ga wasu kamfanonin shigo da magunguna saboda kauce wa ka’ida a cikin ayyukansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.