Nijar

Nijar za ta kaddamar da sabon shirin yaki da ta’addanci

Shugaba Issoufou Mahamadou na Nijar
Shugaba Issoufou Mahamadou na Nijar BOUREIMA HAMA / AFP

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce za ta kaddamar da wani shirin tsaron kasa da zai taimaka mata wajen yaki da ta’addanci a kasar da ke fama da hare-hare.

Talla

A lokacin gudanar da wani taron masana harkar tsaro da manyan sojojin kasar a birnin Yammai, babban jami'i a fadar shugaban kasar Ouhoumoudou Mahamadou ya ce taron shi ne mataki na farko domin tattauna matakan da za a dauka nan gaba.

Jami’in ya ce bukatar su ita ce na ganin sun dinga daukar matakan kariya maimakon mayar da martani.

Jami’in ya bayyana matakan da suka hada da na soji da tsaron cikin gida da yaki da ta’addanci da kuma laifuffukan Internate.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.