Nijar-Amurka

Jiragen Amurka marasa matuka masu makamai sun soma aiki a Nijar

Jirgin yakin Amurka maras matuki kirar MQ-9 a sansanin sojin Amurka da ke Kandahar a Afghanistan.
Jirgin yakin Amurka maras matuki kirar MQ-9 a sansanin sojin Amurka da ke Kandahar a Afghanistan. REUTERS/Josh Smith

Rundunar sojin Amurka da ke kula da nahiyar Afrika ta ce jiragenta marasa matuka sun fara aiki a Jamhuriyar Nijar, bayan samun izini daga kasar wajen amfani da irin jiragen domin yakar ‘yan ta’adda.

Talla

Tun a watan Nuwamba na shekarar 2017, gwamnatin Nijar ta bai wa rundunar sojin Amurka izinin fara amfani da jirage marasa matuka masu makamai, a maimakon marasa makamai da Amurkan ke amfani da su wajen leken asirin ‘yan ta’adda a kasar a shekarun baya.

Kakakin rundunar sojin Amurka a nahiyar Afrika Samantha Reho, ta ce an girke jiragen yakin marasa matuka ne a sansanin sojinsu da ke birnin Yamai, sai dai za a mayar da jiragen kirar MQ-9 zuwa sansanin sojin Amurka da ke Agadez.

Jiragen yakin marasa matuka za su taimakawa Amurka wajen kai hare-hare kan mayakan ‘yan ta’adda a yankunan yammaci da kuma wasu kasashen arewacin Afrika.

Matakin dai ya biyo bayan hallaka wasu sojojin kasar ta Amurka ne da ‘yan ta’adda suka yi a kusa da yankin Iyakar Nijar da Mali farkon wannan shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.